Shugaba Amurka Donald Trump ya tarbi Shugaban Mexico, Andrés Manuel López Obrador a fadar White House a ranar Laraba 8 ga watan Yuli don ganawa akan cinikayya, tattalin arziki da kuma shige da fice, ‘yan kwanaki bayan da sabuwar yarjejeniyar cinikayya tsakanin Amurka, Mexico da Canada ta fara aiki.
"Dangantaka tsakanin Amurka da Mexico ba ta taba yin kusancin da ta ke da shi a yanzu ba," abinda Trump ya fada kenan kafin shugabannin biyu suka sanya hannu a sanarwar hadin gwiwa game da yarjejeniyar a lambun Rose Garden da ke fadar White House.
Firai Ministan Canada Justin Trudeau, bai halarci ganawar ba don bukin sa hannu a yarjejeniyar wadda ake kira USMCA a takaice, ya bada dalilin aiki da kuma rashin dacewar yin tafiya tsakanin kasa da kasa a lokacin da ake fama da annobar cutar COVID-19.
Trump ya ce Amurka mazauni ne ga Amurkawa 'yan asalin Mexico miliyan 36, kuma suna da “babban kaso a bangaren masu kananan kasuwanci na kasar.”
Facebook Forum