Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Ya Ziyarci Gidan Yarin Da Aka Daure Mandela


Shugaba Barack Obama a Afrika Ta Kudu
Shugaba Barack Obama a Afrika Ta Kudu

Shugaban Amurka Barack Obama ya jinjinawa gwarzon yakin wariyar launin fata Nelson Mandela

Shugaban Amurka Barack Obama ya ziyarci tsibirin Robben dake Afrika ta kudu jiya lahadi, gidan yarin da tsohon shugaban kasar Nelson Mandela ya shafe kusan shekaru 20, sabili da yakin hambare gwamnatin mulkin wariyar launin fata.

Mr Obama ya gana da dangin Mr. Mandela wanda ya shafe makonni uku a asibitin dake birnin Pretoria, sabili da cutar hutu da yake fama da ita. Shugaba Obama bashi da niyar ziyartar gwarzon yakin wariyar launin fatar, sai dai yace, karfin halinshi da komawa mulkin damokaradiya da aka yi a Afirka ta Kudu ya karfafa mashi guiwa.

Shugaba Obama ya je Afrika ta Kudu ne a ziyarar mako guda da ya kai nahiyar Afrika da nufin habaka harkokin cinikayya da tattalin arziki.

Banda tattaunawar da ya yi da shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma, jiya asabar, Mr. Obama ya kuma sanar da wani sabon shirin kawo matasa dari biyar kowacce shekara zuwa Amurka domin samun horaswa a fannin harkokin shugabanci.

A halin da ake ciki kuma shugaba Obama ya yi alkawarin kai ziyara kasar mahaifinsa ta gado, Kenya, kafin karshen wa’adin mulkinshi, bayanda ya tsallake kasar a ziyarar kasashen nahiyar Afrika da yake yi a halin yanzu.

Da yake jawabi a wani taron musayar miyau da matasa ‘yan Afrika a Soweto, Afrika ta Kudu, Mr. Obama ya bayyana cewa, zai ci gaba da shugabanci har zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai.

Yace “idan bayan shekaru uku da wata bakwai, ban je Kenya ba, to sai kice ban cika alkawarin da nayi ba,

Shugaba Obama yana amsa tambayar wata mace ne ‘yar asalin kasar Kenya da tayi ta tauraron dan’adam.

Mahaifin Mr. Obama, Barak Obama babba, dan kasar kasar Kenya ne masanin tattalin arziki.

‘Yan kasar Kenya da dama sun bayyana rashin jin dadinsu ganin shugaba Obama ba zai yada zango a Kenya ba a ziyarar mako guda da zata kaishi Senegal da Afrika ta Kudu da kuma Tanzaniya dake kan iyaka da kasar Kenya.

Mr. Obama yace ba daidai bane ya ziyarci kasar a wannan lokacin, yayinda sabuwar gwamnati take kokarin daidaita lamura da al’ummar kasa da kasa.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta wanda aka zaba a watan Maris da kuma mataimakinshi William Ruto dukansu suna fuskantar karar da aka kai gaban kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa, zasu kuma bayyana gaban kotun karshen shekarar nan. Ana zargin mutanen biyu ne da kulla kazamin tashin hankalin da aka yi asarar rayuka bayan zaben shugaban kasa a shekara ta dubu biyu da bakwai.
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG