Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama ya yada zango a kasar Argentina


Shugaban Amurka Obama da shugaban Argentina Mauricio Macri
Shugaban Amurka Obama da shugaban Argentina Mauricio Macri

A kan hanyarsa ta dawowa daga Cuba shugaba Barack Obama ya yada zango a kasar Argentina inda ya gana da shugabankasar mai son akidar kasuwancin jari hujja

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya gana da takwaransa na kasar Argentina, Mauricio (Maurisiyo Makri) Macri, a wata alamar farfado da dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Obama ya sauka kasar da sanyin safiyar jiya Laraba, inda zai yi zirar kwanaki biyu, wadda ta zo daidai da cika shekaru 40 da juyin mulkin da Amurka ta goyi baya.

An karfafa matakan tsaro biyo bayan harin da aka kai a shekaran jiya Talata a birnin Brussels. An rufe wasu daga cikin tashoshin jiragen kasa, da wasu tituna da ke da kusanci da inda shugaba Obama zai ziyarta a Argentinar.

A yammacin jiya Laraba, Obama ya jagoranci wani taro ganawa da matasan Argentina, inda ya amsa tambayoyinsu akan batutuwa masu yawa, da suka hada da batun ta’addanci da kimiyya da ilimi da kuma dangantaka tsakanin Amurka da Argentina.

Shugaban dai yace yana nan kan bakarsa na inganta dangantaka tsakanin al’umma, har ya bayar da missali kan yawan danginsa da suka hada kabilu daban daban da kuma launin fata.

Ya kuma yi magana kan hada kai domin dakile yaduwar cutar Zika. Yace, manufar Amurka ita ce ta yi aiki da kasar Brazil da Cuba da Argentina, domin samun hanyar da za a kawo karshen cutar cikin gaggawa, da samar da maganin da mutane ke bukata.

XS
SM
MD
LG