Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari yace gwamnatinsa zata yi na'am da taimakon OIC


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yau Alhamis Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya fada a Makka kasar Saudiya cewa gwamnatinsa zata yi na'am da taimakon kungiyar hadin kai ta Islama ko OIC a takaice a kokarin sake farfado da wuraren da ta'adancin Boko Haram ya daidaita.

Yayinda yake magana da babban sakataren kungiyar ta OIC Mr. Iyad Ameen Madami Shugaba Buhari ya gargadi kungiyar ta aika da wata tawagar bincike zuwa jihohin Borno, Yobe da Adamawa ta ga irin barnar da kungiyar 'yan ta'adan ta yi.

Shugaba Buhari ya fadawa Mr. Madani cewa tawagar zata taimakawa OIC yanke shawara akan irin taimakon da zata iya ba Najeriya domin farfadowa da sake tsugunar da al'ummomin yankin da suka rasa muhallansu.

Shugaba Buhari ya kara kalubalantar kungiyar ta OIC da ta gaggauta bada taimakonta akan kawo zaman lafiya da tabbatar da doka da oda a kasar Libya wadda yace ta zama kasar da yanzu take da 'yan ta'ada dake haddasa miyagun ayyuka a kasashen yammacin da tsakiyar Afirka tun lokacin da gwamnatin Ghaddafi ta ruguje. Kasar Libya ta zama wata cibiyar harfar da 'yan ta'ada

Shugaba Buhari ya yadda da Mr. Madani cewa 'yan ta'ada dake aikata ta'adanci da sunan addini sun makawa addinin Musulunci wani mugun suna.

Shugaba Buhari yace ta hanyar ilimantar da mutane ne kawai da ingantaccen ilimin addinin Islama zai dakile yaduwar 'yan ta'ada da ta'adanci da sunan Islama. Ingantaccen ilimi ne zai hanasu samun mutane suna shiga kungiyoyinsu.

Saboda haka ya gargadi kungiyar OIC ta taimaki gwamnatin tarayyar Najeriya kawowa kasarsa ilimin gaskiya da wayar da kawunan 'yan Najeriya da gaskiya.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG