Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da barin wasu tankokin man fetur guda dari biyu da cisi'in da biyar shiga Najeriya ba ta hanyar da ta dace ba, kuma ya amince da kiran da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Janar Mohammed Babagana Monguno yayi akan a gudanar da cikakken bincike akan lamarin tare da tabbatar da an hukunta duk jami’an dake da hannu a wannan badakala domin ya zama darasi ga ‘yan baya.
Wannan na zuwa ne bayan da Janar Monguno ya gabatar wa shugaba Buhari rahoton binciken da wani kwamiti da ya kafa a ofishinsa ya gudanar dangane da lamarin da ya shafi karya dokokin Najeriya da na kasa-da-kasa, musamman batun shigowa da man fetur daga ketare ko kuma fitar da shi daga Najeriya zuwa waje.
A wata hira da Muryar Amurka ta yi Janar Abdulrazak Umar mai ritaya, mai sharhi kan lamarin tsaro ya fadi cewa akwai bukatar mutane masu tsoron Allah da sanin ya kamata, masu kishin kasa kuma, su gudanar da binciken don bankado duk wani yinkurin rufa-rufa in ba haka ba binciken zai zama da wahala, domin a cewarsa tabbas masu hannu a wannan aikin zasu yi kokarin yin rufa-rufa don kare kansu.
Shi ma Ibrahim Katsina, tsohon jami’in tsaro a Najeriya, ya yaba da kokarin da gwamnatin Buhari ke yi don gano wadanda suka aikata wannan danyen aikin da ya kira “cin amanar kasa". Ibrahim Katsina ya kara da yin kira kan tabbatar da zaman lafiya a kasa, ta hanyar hukunta masu laifi don ya zama abin koyi ga na baya.
Ga karin bayani cikin sauti.