Shugaban Amurka Barack Obama, yayi amfani da jawabin daren Talata na halin da kasa ke ciki karo na uku, wajen bayyana sabbin matakan da Gwamnatinsa ke dauka domin bunkasa tattalin arzikin Amurka.
Jawabin halin da kasa ke ciki karo na uku da shugaban Amurka Barack Obama ya yiwa Amerkawa daren Talata, yazo ne a daidai lokacin da ake dab da fara gangamin yakin neman zaben shugaban kasa.
Zaben da shima Barack Obama ke neman a sake zabensa domin zagaye na biyu.Ya yi kira ga ‘yan majalisar dokokin Amurka da a rika kauda kai daga bambancin ra’ayin siyasa, a rika duban yiwa kasa aiki maimakon sanya muradun jam’iyyar “Democrat ko Republican” a gaba.
A jawabin na shugaba Barack Obama ya kuma karfafa bada karfi kan sabbin hanyoyin da Gwamnatinsa ke dauka domin bunkasa tattalin arzikin Amurka ya zama mai karfi. Yace za’a gudanar da sauye-sauaye masu karfi da zasu dore wajen bunkasa tattalin arzikin Amurka.
Ya kuma karfafa cewar ya kamata Amurka ta kasance a sahun gaban kasashen da za’a yiwa sha’awar zama ayi aiki, amma ba kasar da attajirai da manyan kasuwa ne kawai zasu ci gaba da yin kane-kane cikin al’amuran kasa amma su talakawa na fama da matsalar halin zaman rayuwa ba.Shugaban na Amurka Barack Obama ya kammala jawabinsa da yin shagube ga ‘yan majalisar dokokin Amurka da suyi koyi da sojin Amurka wajen hada kai doin yiwa kasa aiki tare da tare da nuna wani bambancin siyasa ba.
Shugaba Barack Obama ya kuma karfafa bayanin daukan kwararan matakan bunkasa ilmi, da yin kwaskwarima kan dokar shige da fice, za’a kuma tabbatar da ganin shiga jami’a a Amurka ta zama mai sauki wajen biya ga dalibai, maimakon a zuba ido karatun jami’a na neman ya gagari ‘ya’yan talakawa ba.Shugaba barack Obama ya kuma yi kira ga Majalisar dokokin Amurka da su rika bada karfi kan tattaunawa da samar da hanyoyin saukaka halin zaman raayuwar Amerkawa ba maida hankali kan zurfin aljihunsu ba.
\Da ya juna kan batun samun makamashi da samar da man fetur kuwa, shugaba Barack Obama yace ya baiwa dukkan jami’an Gwamnatin Amurka da abin yafi shafa umanin da su bude ma’ajiyar mai da iskar gas da Amurka ke dasu domin samar da isasshen mai ga kasuwannin Amurka tare da hana farashinsa hauhawa a kasuwa.
Shugaba Barack Obama ya kuma tunawa Amerkawa muhimman ayyukan da Gwamnatinsa tayi zuwa yau, wadanda suka hada da kauda Osama Bil Laden da daukan matakan kauda iska mai gubar da masana’antun Amerkawa ke watsawa a sararin samaniyar Amurka.