Muryar Amurka ta tambayi kakakin sojojin Najeriya Birgediya Sani Kukasheka yiwuwar kama Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram cikin wa'adin da Janar Yusuf Tukur Buratai ya ba sojoji.
Inji shi kakakin sojojin suna kan aikin kuma zasu cika wa'adin. Yana mai cewa akwai wadanda walau sun ga wuta ko kuma sun fahimci cewa akidar Boko Haram ta banza ce saboda haka suka mika kai.Suna ganin an yi masu karya an yaudaresu.
Hadimin mukaddashin shugaban Najeriya Hafisu Ibrahim yace gwamnatin Najeriya nada kwarin gwuiwa akan sojojin.
Dangane da cewa umurnin tamkar an riga malam Masallaci ne sai ya ce ba'a yi ba. Yana mai cewa aiki ne na jami'an tsaro. Sun san abun da zasu yi domin cimma nasara. Janar Buratai da ya bada umurnin ya san abun da ya taka. Watakila yana da bayanan sirri da zai yi anfani dashi.
Aliko Harun wani tsohon hafsan leken asiri na soja yace harkar tsaro na bukatar sirri. Ba komi ya kamata a fito a fadawa jama'a ba.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum