Yayin da ake ci gaba da karawa a gasar cin kofin duniya ta mata a Faransa, a yau kungiyar kwallon kafar kasar Kamaru za ta fatata da Canada a wasanta na farko.
Hankulan masu bibiyar gasar ta mata a nahiyar Afirka, sun karkata kan kasar Kamaru, wacce za ta buga wasanta na farko a yau.
Kasashen Kamaru, Najeriya da Afirka ta Kudu ne kadai suka samu damar halartar gasar ta cin kofin duniya..
Sai dai Afrika ta kudu ta sha kaye a hannun Spain da ci 3-1 a wasanta na farko yayin da ita ma Najeriya ta kwashi kashinta a hannun Norway inda aka lallasa ta da ci 3-0.
Kamaru, Canada, Netherlands da New Zealand na rukunin E ne a wannan gasa.
‘Yar wasan Kamaru da za a zuba ido akanta, wacce ita ce tauraruwar tawagar ‘yan wasan ita ce, Gaelle Enganamouit yayin da Canada ke tunkaho da kyaftin dinta Christine Sinclaire.
Facebook Forum