A ranar 20 ga watan Yuli na shekarar 1969, kimanin shekaru 50 kenan da hukumar binciken sararrin samaniya ta Amurka NASA ta tura mutane karon farko zuwa duniyar wata da ake kira “Apollo 11”. Mr. Neil Armstrong da Edwin Aldrin suka fara zuwa duniyar.
Su ne mutane na farko a tarihin duniya da suka fara shiga kuma suka yi tafiya a cikin duniyar wata. A bana hukumar na bikin cika shekaru 50 da yin wannan jan aikin mai cike da tarihi. Hukumar ta inganta dakin da aka girke na’urorin da aka yi amfani da su wajen aikawa da magana da mutanen biyu a yayin da suke cikin duniyar.
A karon farko da aka bude dakin kuma aka inganta shi da na’urorin zamani, duk da cewar an sake maida dakin kamar yadda yake a waccar shekarar ta 1969, wanda ya yi kamar masu aikin sun dan fita shan iska, wanda ake so a nuna yadda yake a lokacin bayan shekaru 50 da suka gabata.
Yanzu haka dai an maida dakin ya zama wani gidan tarihin kunbo afolo 11 da aka sani.
Facebook Forum