Yayinda ake ta bankwana da shekarar 2014, jama’a na fatan shiga sabuwar shekara lafiya da kuma ganin bayan ta lafiya.
Malam Balarabe Rufa’I wani matashi ne da Dandalin Muryar Amurka ya zanta da shi dangane da tsammaninsa na sabuwar shekara, inda yace Najeriya na fuskantar zabe a shekar 2015, kuma ga sauyin kudin man fetur da aka samu a duk fadin duniya, abinda tattalin arzikin kasar ya dogara gashi.
A zabe mai zuwa, Najeriya na neman shugabannan da zasu zo da tsare-tsaren dasu kawo habbakar tattalin arzikin kasar, amma sai ya kasasnce, zaben na cike da fargaba saboda a wannan karon an shigo da siyasar addini, da kabilanci da kuma batanci.
A cewar malam Balarabe Rufa’I, mutane na ganinn cewa, zaben shekarar 2015 zai sa inda alkiblar Najeriya za ta dosa. Ya kuma yi kira ga shugabannan addinai dasu ja wa al’ummominsu kunne da su cire batun addini a harkokin siyasar Najeriya. Ya kuma yi kira ga hukumomin gwamnati dasu tsaya su yi aikin su tsakani da Allah ba tare da karkata zuwa ga harkar siyasa ba.