Matakan sun hada da haramta ‘yan rakiya ga matafiya da rage kujerun dake cikin jirage domin hana cunkoso baya ga tsaftace jiragen sama da ofisoshin dake tashoshin ta hanyar amfani da sinadaran kashe kwayoyin cuta.
Ya zuwa yanzu dai hukumomin dake gudanar da aikace aikacen su a filayen jiragen sama sun dukufa tanade tanaden cika sharrudan da hukumomi suka shimfida.
Hukumar NDLEA na cikin hukumomin dake mu’amala ta kai tsaye da fasinjoji a tashar jiragen sama kuma Muhammad Ajiya shi ne kwamandan hukumar mai kula da tashar jirgin sama ta Malam Aminu a Kano kuma ya bayyana wa Muryar Amurka irin matakan da suke dauka a nasu bangaren.
“Mun tanada wa ma’aikatanmu safar hannu saboda aikinmu ya kunshi taba kayyaki da kuma jikin mutanemutane .”
Batun rage kujerun cikin jirgi na daga cikin sharrudan tabbatar da tazara tsakanin fasinjoji, a cewar hukumomin da ke kula da tashoshin jiragen sama a kasar.
Engr Adamu Muhammad Adamu dake zaman manajan tabbatar da ingancin ayyuka da kare lafiyar fasinjoji na kamfanonin jiragen sama na MAX AIR ya ce “abu ne mai wahala jirage su iya bayar da damar bada wannan tazara ta mita 2 da kuma rage kujeru.”
Wani kalubale da masana a fannin sufurin jiragen saman Najeriya ke ganin za’a fuskanta a yanzu shi ne karancin matuka jiragen, saboda wa’adin takardun wasu daga cikinsu na shaidar tuka jirgi ya kare kuma basu kai ga sabunta su ba saboda annobar Korona.
Masu kula da lamura dai na ganin sake bude tashoshin jiragen saman Najeriyar ka iya zama tafarkin tada komadar harkokin tattalin arzikin kasar wadda annobar Korona ta kara raunana shi.
Facebook Forum