Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauyin Shekar 'Yan Siyasa Bai Zama Alheri Ga Demokaradiyya Ba


Kwamrade Sagir
Kwamrade Sagir

Kwamarad Sagir -- Ya kamata masana su shigo cikin harkar siyasa domin tsaftace demokaradiyya a Najeriya, baya ga samar da ilimin da ya dace, a cewarsa matsalar mulki a Najeriya itace ta ganin kyashin juna wala Allah ta fannin addini ne ko al’ada.

Lokaci yayi da matasa zasu tashi tsaye su nemawa kansu mafita domin babu wani mahaluki da zai kawo masu maslaha, yace ya kamata a yi wa harkar mulki kallon tsanaki domin ceto kasar nan.

Ya kamata a samar da hurumi na ilimi ya wadata a 'kasa, sannan idan za’a samu wadanda zasu yi mulkin Najeriya, tare da samar da tsaro ne kasar nan zata kara da sauran kasashe.

Sagir, ya kalubalanci matasa da ma sauran 'yan Najeriya da sai an sami mai mulkin da zai samar da wadannan abubuwa na more rayuwa ne, kafin a zabe shi tare da duba a baya me wannan dan takara yayi wa al'ummarsa na ci gaba, ba kawai ya zo yana cewa zanyi kaza da kaza ba.

Ya bayyana cewar Najeriya ba ta rasa wadanda zasu yi ayyukan azo a gani ba muddin za’a basu dama domin kawo canji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:50 0:00


  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG