Wata sabuwar fasahar salon sauya fasalin kwayar hallitar sauro domin kawar da zazzabin cizon sauro wato Malaria, wanda yake hallaka Akalla mutane 429,000 a kowace shekara mafiyancin su yara ne ta ja hankali kwarai.
Masana Kimiyya daga kwalejin da ake kira, Imperial College London, sun fito da wata sabuwar fasaha da za a kawar da kwayar halittar sauro a dakin binciken magunguna (laboratory) ta hanyar amfani da sabuwar fasahar da ake kira da Gene Drive. Wannan hanya ce da zata hana macen sauro hayayyafa kuma zata kashe dukkan kwayar hallitar Sauron da ake gwaji a kansu.
Wadannan masana Kimiyya na fatan zasu yi amfani da sabuwar fasahar daga dakin bincike zuwa daukacin duniya domin yakar zazzabin cizon sauro.
Farfesa Andrea Crisanti, na Imperial College London, ya bayyana yadda fasahar take inda ya ce za a dauka kwayar hallittar Sauron da ke dauke da jinsin mace sai a gurbatashi ta yadda bazai taba iya zama jinsin mace ba, amma zai iya zama wata halitta daban kamar tsakatsakiya wanda a turance ake kira da INTERSEX ita wannan haliita zata kasance wadda bata iya cizo, bata iya kwai kuma ba zata iya hayyayafa ba.
Masana Kimiyya zasu Inganta wannan fasahar domin dattabar da lafiyar
Al’umma yayin da za a yi gwajin a cikin shekaru biyar zuwa goma masu zuwa domin ya zamto daya daga cikin hanyoyin yaki da cutar cizon sauro wato Malaria.
Facebook Forum