Yanzu dai a filin ne cewa 'yan ta'ada a Nigeria sun canja dabarun tada bama bamai da kuma kai hare haren kunar bakin wake.
Wasu masana suna da ra'ayin cewa na'urorin da ake amfani dasu daga nesa na sunsuno bama bamai a tashoshin mota da kasuwani da kuma wasu wuraren da ake samun cunkuson jama'a ba zasu taimaka yadda ya kamata
Sun yi bayanin cewa ana bukatar na'urorin zamani domin kare jama'a da kuma suma jami'an taro da suke aikin kare lafiya da dukiyoyin jama'a.
Karuwa hare haren kunar bakin wake na tado karin bukatar mutane su rage tsoro wajen kula da shige da ficen wadanda basu yarda da take taken su ba
A ziyarar da shugaba Buhari ya kai Kamaru, ya kara karfafa batun daukan matakan hana ta'adanci akan iyakokin kasashen dake makwaptaka da tapkin Chadi.
Masana na nuni da cewa yan ta'ada sun watsu zuwa garuruwa a halin yanzu, da hakan ke kawo karin hare haren sari ka noke.
Tsohon shugaban madatsar mai ta Kaduna Injiniya Kailani Mohammed yana ganin sauya dabarun tsaro a yankunan da mutane ke taruwa zai fi zama a'ala