An gudanar da wannan binciken ne a jami’ar jihar Michigan ta Amurka.
Binciken da aka buga a wata mujallar kimiyya, ya nuna wannan kwayar cutar da kyar take rayuwa a sauron dake dauke da wannan kwayar cutar.
Bisa ga rahoton, yaduwar cutar zazzabin cizon sauro tsakanin mutane ta wurin irin wannan sauron zai rage yaduwar cutar tsakanin mutane.
Masana sunce wannan ne karon farko da za’a samu karuwar rage yaduwar cutar malariya.
Sauro mata suna yada kwayar cutar maleriya ne ga ‘ya’yansu mata, wadansu lokuta, kwayar cutar tana sa sauron haihuwar mata sosai.
Zazzabin cizon sauro shine cutar da tafi kashe mutane a duniya. Hukumar lafiya ta duniya ta yi kiyasin cewa, kimanin mutane miliyan 220 suke kamuwa da zazzabin cizon sauro kowacce shekara 660,000 kuma suke mutuwa ta dalilin cutar.