Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Ingila Ta daure wani Yeriman Kasar Saudi Arabiya Shekaru Ashirin,Saboda Kisan kai.


Hoton shari'ar yeriman Saudi Arabiya da aka yankewa hukuncindaurin shekaru ashirin
Hoton shari'ar yeriman Saudi Arabiya da aka yankewa hukuncindaurin shekaru ashirin

Laraba ce Kotu ta sami Yerima Saud Abdulaziz bin Nasser, da laifin kashe dan gidansa,wanda ya yi wa dan karen duka,ya kuma shake shi lahira.

Wata kotun Ingila ta yanke wa wani Yeriman Saudiyya daurin akalla shekaru ashirin a gidan yari, saboda samunsa da lifin ya yi wani dan gidansa duka ya kuma shake shi har lahira.

Yau laraba ce wani alkali ya gayawa Yerima Saud Abdulaziz Bin Nasser, cewa babu wanda ya fi karfin doka.

Cikin watan febwairu ne aka sami gawar Bandar Abdulaziz,a O’tel. Yerima Saud ya amsa laifin zama sanadiyyar mutuwar ajali,amma bai ayyana kashe shi ba.

Masu gabatarda kara sunce an lakadawa mamacin dan Karen duka,kuma irin raunuka da aka gani a jikinsa da alamun an far masa da nufin kwana da shi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG