Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Satar 'Yan Matan Chibok Ta Shiga Shekara Ta Shida


Wani taron masu fafutukar ganin an saki 'yan matan Chibok
Wani taron masu fafutukar ganin an saki 'yan matan Chibok

Iyayen ‘yan matan makarantar sakandaren Chibok da suka rage hannun ‘yan ta’addan Boko Haram suna cigaba da kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran mahukuntan Najeriya su taimaka su kwato musu ‘ya’yan su.

Kimanin shekaru shida kenan da aka sace ‘yan matan a garin Chibok da ke arewa maso gabashin Najeriya a wani samame da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai a makarantar sakandaren a shekarar 2014 kana suka yi awon gaba da ‘yan mata 220.

A cikin shekarar 2017 ne hukumomin Najeriya suka karbo wasu a cikin ‘yan mata a wata musayar da gwamnatin ita ma ta saki wasu ‘yan kungiyar Boko Haram.

Ya zuwa yanzu akwai ‘yan mata da suka kai 112 da suka rage a hannun ‘yan ta’addan ba tare da sanin makomarsu ba.

Mrs. Rebecca Samuel mahaifiyar daya a cikin ‘yan matan da suka rage hannun ‘yan Boko Haram ta yi kira ga shugaban kasa da ya kara azama a kokarin kubutar da ‘yan matan.

Ta kara da cewa tana sane da kokarin da hukumomin gwamnati ke yi a kan wannan batu akwai bukatar kara kaimi.

Rebecca ta ce tana fuskantar kunci a rayuwarta da yawan tunani na rashin ‘yarta amma ta ce tana addu’a duk lokacin da za ta shiga bacci.

Mrs. Rebecca Samuel ta yi wadannan kiraye kirayen ne a wata hira da ta yi wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Abuja, Sale Shehu Ashaka.

Hukumomin Najeriya dai a baya, sun sha fadin cewa suna iya bakin kokarisu wajen ganin sun kubutar da 'yan matan da suka rage.

Ga cikakkiyar kuma hira da suka yin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG