Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, da abokin hamayyarsa mai ra’ayin gurguzu Francois Hollande, sun kara a mukabala daya tal da suka yi gabannin zaben fidda gwani da za a gudanar ranar Asabar, zabe da ake kyautata zaton Hollande ne zai sami nasara.
A lokacin muhawarar da aka nuna ta talabijin a jiya laraba,Mr. Sarkozy ya zargi Mr.Hollande da shirga kariya gameda manufofin tattalin arziki a lokacin da suke sa in sa. A nasa bangaren Mr. Hollande, ya zargi Mr. Sarkozy da kin daukar alhakin kasa karfafa tattalin arziki da samar da ayyukan yi da ake matukar fuskanta da ma wasu matsaloli da Faransa take fama da su ahalin yanzu.
Kuri’un neman jin ra’ayin jama’a suna nuna Sarkozy yana baya da maki 6-10. Mr. Hollande ne ya zama dan takara da yake kan gaba, bayan kammala zabe zagaye na farko. Mr. Sarkozy yana shan suka dangane da matakan tsuke bakin aljihu masu tsanani da ya aiwatar, da nufin rage bashi da Faransa take fama da su.