Shugaban kwamitin shirya zabe na hukumar kwallon kafa ta Najeriya. Sani Katu, yayi watsi da jita jitan da ake yi cewa kwamitin ya kammala shirye-shiryensa da zai hana bada dama ga wasu manyan masu takara shiga zaben neman shugabancin hukumar NFF da za a gudanar cikin wannan watan.
Wata majiya da ta ce bata son a ambaci sunanta ta fada wa kamfanin dillancin labarai (NAN) cewa an kammala shirye-shiryen hana tsohon shugaban Hukumar NF, Aminu Maigari, da kuma shugabanta na yanzu Amaju Pinnick, shiga takarar.
Shirin shine za'a cerisu a wajan tantancewa inda za'a bar mutum daya kawai wato Taiwo Ogunjobi kasancewar bashi da jama'a a cikin masu jefa kuri’a.
Bayan an kammala tantance 'yan takarar, kwamitin zabe zai bada damar sake sayen takardun neman izinin takara na tsawon kwanaki biyar don samun damar karin mutane da zasu fafata a karshe inda za'a sanya Shehu Dikko, Shugaban Harkokin Gudanarwa cikin takarar.
Sai kuma daga karshe su kara tsakanin su Ogunjobi, sauran 'yan takarar masu ra'ayin' takara daga yankunan za'ayi waje dasu daga karshe kamar yadda ake fada.
Amma Sani Katu, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) cewa kwamitin ba shi da wani shiri don hana wani tsayawa in har ya cika kaidojin takardun ne da ake bukata.
Ya ce tuni ma mun riga mun gama tantance 'yan takara kuma za mu ci gaba da taron mu a ranar (Litinin) don sanin mataki na gaba.
Duk da haka, ya ce akwai yiwuwar canje-canjen lokacin aiyuka na zabe idan an bukata amma za a yanke shawara a taron da kwamitin ya shirya a ranar litinin.
Inda za wallafa sunayen 'yan takara na karshe a ranar 7 ga watan Satumba kuma za a gudanar da zaben na NFF, wadda zai jagoranceta daga 2018 zuwa 2022, a watan Satumba nan da muke ciki.
Facebook Forum