Zainab Safyanu Abdulmalik – wadda ta kammala karatunta a matakin digiri na farko a fannin Kwamfuta (Computer), bayan ta shafe shekaru hudu tana neman gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ta nemi fannin karatun Bio Chemistry, bata samuba daga karshe, Allah ya bata sa’a ta samu gurbin karatu a Jami’ar Bayero ta Kano.
Lokacin da ta fara karatu, ta fuskanci kalubale, saboda ba abunda ta so ta samu ba ne. Ta so ta fito da makin First Class, amma hakar ta bata cimma ruwa ba. Ta dai yi kokarin kammala karatunta ba tare da ta fuskanci wata matsala ba.
Da ta kammala karatun ta, sai ta kama sana’ar hannu, inda ta fara koyon harkar kwaliya. Kasancewar samun aiki a yanzu sai mutum nada wanda ya tsaya masa.
Ta kuma koyi harkar make-up ne ta fannin amfani da shafin sadarwa na Youtube, inda daga nan ta samu aiki a gidan wani daukar hoto, tana yi wa wadanda suke daukar hoto kwaliya.
Ta kara da cewa sana’ar hannu itace maslaha ga matasa. Karatu na da kyau, amma sana’ar hannu itace mafita, ko da kuwa matashi na aikin gwamnati ko na kamfani sana’ar hannu, abin dogaro da kai ne.
Facebook Forum