Kamfanin Samsung ya sanar da dakatar da fitar da sabuwar wayar shi mai budewa da kullewa, da aka shiryar da fitar da ita a kasuwa jiya Litinin.
Kamfanin ya bayyanar da dalilinsa na dakatar da fitar da wayar da cewa, bayan an kai wayar wajen wasu masu duba inagaci da nagartar wayar sai suka ga cewar wayar nada matsalar skirin, wanda hakan babbar matsala ce idan aka fitar da ita a kasuwa.
Sabuwar wayar ta Galaxy Fold ba zata fitoba har sai an gama bincikar halin da take, kamfanin yace wasu masana sun bashi shawara akan hanyoyi da za’a bi don inganta wayar ta shiga kasuwa don gagarar kowace irin waya.
Kamfanin yace zai sanar da ranar da za’a fitar da wayar kasuwa nan bada jimawa ba. Ana sa ran kudin wayar zai fara daga dallar Amurka $1,980 kwatankwacin naira dubu dari bakwai N700,000.
Facebook Forum