An danganta rashin daukar matakan da suka dace wajan kula da yara dake sansanin ‘yan gudu hijira a arewa maso gabashin Najeriya, a matsayin abinda ke haifar da halin da yara suke ciki na rashin abinci mai gina jiki.
Tsohon, shugaban hukumar agajin gaggawa na jihar Borno, Malam, Grema Terab, ne ya bayana haka a shirin Muryar Amurka, na yau da gobe, inda yake cewa kungiyoyin agaji na duniya ne ke rike da yawanci sansanonin inda suke taka rawar gani.
Ya kara da cewa alokacin yakin neman zabe da ‘yan siyasa ke zawarcin ‘yan gudun hijira shanu da kaji basu yankewa a sansanonin, amma tunda hakarsu ta cimma ruwa ba a ko ganin keyarsu a sansanonin.
Malam Terab, yana me cewa yakamata gwamnatin ta dauki mataki na magance yawan mace mace a sansanonin ‘yan gudun hijira, da kuma sa ido akan kayayyakin agaji da gwamnati da kuma sauran kungiyoyi masu zaman kansu ke kaiwa sansanonin.
Ya ci gaba da cewa satar da yi sama da fadi da kayayyakin talafin ‘yan gudun hijira ba karamar illa yakewa sansanonin ba.