Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salon ‘Yan Boko Haram Na Canzawa-Inji Wasu Shugabannan Matasa.


Batun tsaro a Najeriya na kara jan hankalin jama’a musamman ganin yadda ‘yan boko haram ke sabunta salon hare harensu.

Cikin ‘yan kwanakin nan dai maharan su kan yi amfani da kananan yara da mata wajen kai hare harensu. Akan wannan batun ne yau Dandalin VOA ya zanta da wasu shugabannan matasa daga arewa maso gabashin Najeriya, Mr Tom Garba da Malam Kabiru Gwangwazo.

Mr. Tom Garba ya fadi cewa a koda yaushe masu irin akida kamar ta boko haram, su kan yi abubuwan da jama’a za su yi Allah wadai da su, shi ya sa su ke badda sahun yadda suke gudanar da al’amuransu. Ya kuma ce, bisa ga hare haren ‘yan kwanakin nan da maharan su ka kai, za a iya cewa su na auna wuraren ibadu ne kamar Choci-Choci da Masallatai.

Mr. Tom ya kuma yi kira ga jama’a da su sa ido, don tsaron kasa ba a kan hukummomi kadai ya rataya ba, jama’a su ma su na da ta su gudunmuwar.

Shi kuma Malam Kabiru Gwangwazo cewa ya yi, masu iya Magana dai sun ce “idan ruwa ya karewa dan kada, sai ya fito gari ya ce shi kadangare ne. Ya ce duk lokacin da wata kungiyar ‘yan tawaye, da ta yi karfi amma ta rasa wannan karfin, sai ta koma yakin sari-ka-noke don jama’a su yi tunanin cewa har yanzu tana nan da karfin su. Wannan yaki na sari-ka-noke dai an dade ana yin shi a tarihin duniya, kuma yawancin lokuta bangaren da aka fi karfi su ke yakin sunkuru a cewar Malam Kabiru. Shi ya sa yanzu 'yan boko haram suka fito da salon yin amfani da yara da mata wajen kai hare haren kunar bakin wake.

Ga Karin bayani daga Ibrahim Abdul’aziz wakilin sashen Hausa.

XS
SM
MD
LG