Kamar yadda aka saba cikin kowane watan Azumin Ramadan, bana ma dan jarida mai zaman kansa a kasar Sudan, Salman al-Parisi, ya shigo cikin zauren "A Bari Ya Huce" domin yi wa masu sauraron filin fashin bakin wasu wakoki.
A kashin farko na wannan fashin bakin da yayi ranar asabar 28 Yuli, 2012, watau Ramadan 9, 1433 Hijr, Salman yayi magana kan wakokin da suka hada da "Ba'adal Layl" da "Ahmad Nabiyyina" wadanda 'yan kungiyar Firqatul Sahwa Lil Intajil Fanni suka rera.
Shi dai malamin yayi zama, yana kuma da alaka sosai da garin al-Zariba ta marigayi Sheikh Abdur-Rahim Muhammad al-Bura'i, wanda ya rubuta akasarin wadannan wakoki tare da sauran shehunan malamai dake wannan gari na al-Zariba.
A saurari kashin farko na wannan hira a cikin shirin "A Bari Ya Huce..." na ranar Asabar 28 Yuli 2012.
Shirin A Bari Ya Huce Salman A Kan Faifan Ba’adal Layl |