Daruruwan mutane suka taru a gidan Alhaji Abu Dan Kure lokacin da labarin sakinsa ya bazu cikin birnin Sokoto. An ga dan kasuwan ne ranar Litinin da dare a unguwar tsohon filin saukar jirgin sama cikin garin Sokoto.Nan ne wadanda suka saceshi suka barshi kana suka gudu.
Shi Alhaji Abu Dan Kure ya ce baya da masaniya kan dalilin da ya sa 'yanbindigan suka sace shi. Bayan sun kamashi sai suka kaishi wani gari da idanunsa rufe. A garin da suka kaishi sun ajiyeshi a wani gida inda ya tarar da wasu da dama su ma suna tsare. Bai san iyakacin mutanen dake tsare ba. Ya ce da suka kamashi sun nada masa rawani da tep suka rufe idanunsa ta yadda ba zai san inda yake ba.
Yayin da suka rikeshi ya ce babu wata azaba ko zagi da suka yi masa. Cikin 'yanbindigar akwai Musulmai akwai kuma Kristoci. Idan lokacin sallah ya yi sai su sa mutane dake Musulmai su yi sallah har da su 'yanbindiga. Suna rikeshi ne zuwa inda zai yi sallah kana in ya gama su maidashi inda suka ajiyeshi.
Basu gaya masa dalilin da ya sa suka sace shi ba. Game da dalilin da ya sa suka dawo da shi Abu Dan Kure ya ce addu'a da yaddar Ubangiji suka sa hakan. Da aka tambayeshi ko 'yanbindigan sun bukaci wasu abu a hannunsa sai ya ce shi da yake tsare bai sani ba. To sai dai lokacin da duk 'yanbindiga suka sace mutum sukan bukaci a biyasu wasu kudade kafin su saki mutum.
Iyalan Dan Kure sun musanta biyan kudin fansa. Nura Abu Dan Kure, daya daga cikin 'ya'yan dan kasuwan ya ce ba gaskiya ba ne cewa sun biya fansa.
Satar mutane da yin garkuwa dasu abu ne da ba saban ba a jihar Sokoto. Wannan ne karon farko.
Murtala Faruk Sanyinna na da rahoto.