Kerry ya ziyarce hedikwatar Kungiyar Tarayyar Afirka a babban birnin na Habasha don tattaunawa da jami'an game da matsalar Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya, inda Musulmi ke cigaba da mujewa daga gidajensu don kauce ma hare-hare daga mayakan sa kai na Kirista.
Da safiyar yau Alhamis din ya gana da Ministacin Harkokin Kasashen Waje na Habasha da Uganda da Kenya don tattaunawa kan yadda za a iya shawo kan bangarorin da ke yaki da juna a Kudancin Sudan su tsaida da mummunan yakin da su ka yi watanni su na yi.
Manyan jami'an na diflomasiyya sun tsai da shawarar cewa lallai Sudan Ta Kudu na bukatar sojoji na hallal su kawo kwanciyar hankali a kasar.