Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ke Spain, ta ce ba ta aikata wani laifi ba yayin da ake zargin ta bari wani dan wasanta da aka haramta mai buga wasa ya buga mata kwallo a gasar Copa del Rey.
A makon da ya gabata aka zargi Juan Chumi Brandariz mai shekaru 19 da buga mata wasa, wanda aka dakatar daga buga kwallo har sau biyu saboda alkalin wasa ya dauki sunansa har sau biyar bayan da aka same shi da laifi.
Amma duk da haka, rahotannin da kafafen yada labaran kasar Spain sun ce Chumi ya bugawa Barcelona wasa a zagayen farko na ‘yan 16, inda Barcelonan ta doke Levante da ci 2-1 a makon da ya gabata.
Kungiyar ta Barcelona ta ce ita ta dauka manyan laifuka ne ke hana dan wasa buga kwallo, a gasar wasannin kasar, tana mai cewa ba ta dauka rubuta sunan dan wasan da alkalin ya yi zai sa a hana shi buga wasa ba.
Jaridun kasar ta Spaniya sun ruwaito a yau Alhamis cewa dakatar da Chumi daga gasar kasar a mataki na uku, ya zama ba zai iya buga wasa ba, saboda haka, za a iya fitar da kungiyar ta Barcelona daga gasar saboda ta take doka.

Facebook Forum