Duk da kokarin da hukumomin tsaro keyi a Najeriya na kawo karshen garkuwa da mutane da ake ta yi a sassan kasar daban daban, har yanzu masu garkuwa da jama’a a kasar na cigaba aika-aikarsu da kuma yin fito na fito da hukumomin tsaron.
A yayin da matsalar sace mutane ta fi kamari a yankin arewacin kasar,
yankunan jihohin yanmacin Najeriyan ma dai ba’a barsu a baya ba, inda ko a
ranar asabar dinnan wasu yan bindiga su ka yi awon gaba da babban jami’in
Hukumar Kashe Gobara a jihar legas, Mr Rasaki Misbau da wasu mutane
6 akan hanyar Epe zuwa Ikorodu da ke jahar legas.
A sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar legas ta raba wa manema labarai
ta hannun kakakinta DSP Bala Elkana, ta ce tuni kwamishinan ‘yansandan
jihar legas, Alh. Zubairu Muazu - tare da marawar wasu kwamandojinsa ya
ziyarci yankin da aka sace mutanen, tare da shan alwashin kama miyagun da
kuma kubutar da wadanda aka sacen don kare rayukansu.
Alh Usman Alfa Shatiman Lapai, wani tsohon jami’in tsaro a Najeriya, wanda Babangida Jibrin ya tambaye dalilin da ya sa harkar tsaro, musanman batun garkuwa da mutanen, ya ki ci ya ki cinyewa, sai ya ce akwai alamun rashin hadin kai ko musayar bayanan sirri a tsaknin rundunonin tsaro daban-daban da ake dasu a kasar, lamarin da ke sa ‘yan ta’addan ke samun damar aikata muggan laifuka
a titunan kasar ba tare da an magance su ba. Ya ce dole ne gwamnati ta
tashi tsaye wajen samar da horo ga jami’an tsaronta domin tunkarar wannan
al’amari cikin gaggawa.
Domin kawo karshen wannan matsalar dai tuni malaman addinai daban-daban
suka fara kira ga mabiya da su tashi tsaye wajen addu’oi, kamar yadda Dr
Bashir Yankuzo, wani malamin addinin musulunci a Najeriya, shi ma ya jaddada.
To ganin yadda ake zargin Fulani da hannu wajen sace mutane ko garkuwa
da su ya sa Babangida ya tambayi wani bafilatani, mai suna Baba Sani, mafita ko
shawara ga Fulanin yan uwansa. Malam Baba ya ce akwai bukatar Fulani da
aka sani a Fulako su daina wannan aika-aikar, tare da kira gare su da su
fito da kuma rungumar sana’o’in kwarai da aka sansu da shi.
Ga Babangida Jibrin da cikakken rahoton:
Facebook Forum