Cikin matasa uku da aka ce sun yiwa Aisha 'yar shekara 14 fyade rundunar 'yansanda ta bayyana matasa biyu a bainar jama'a. Kakakin 'yansandan Mr. Richard Adamu ya ce a yanzu yara biyu ne bincikensu ya nuna suka aikata wannan ta'asar. Amma kuma daya ne ya yi anfani da ita bayan ya sa wata kwaya cikin kunun zakin da ya bata.
Wakilin Amurka wanda yake bin maganar sau da kafa tun lokacin da abun ya faru ya zanta da matasan wadanda 'yan shekaru 18 ne a duniya. Ahmed Zakari daga Kontagora ya ce ya san abun da ya kawo shi hannu 'yansanda. Ya ce a kan yarinyar da suka yi anfani da ita ne. Ya ce sun sayi kunun zaki kashi biyu. Sun sha daya amma sun sa kwaya cikin daya wanda suka bata ta sha. Daga nan ne abun ya faru. Ahmed Zakari ya ce bayan ya yi anfani da ita sai ya ga ta fara juye-juye.
Na biyun Rufai Umar shi ma daga Kontagora ya ce a dakinsa aka yi ta'asar. Ya ce lokacin da suke tare ya barsu a dakinsa domin lokacin zuwa horon koyar buga kwallon kafa da yake zuwa ya yi. Daga filin kwallon ne aka fada masa ana neman sa. Ya ce yana zuwa wata mata a cikin gidansu ta ce ana bidarsa. Yana kan gudu zuwa gida ya gamu da Ahmed Zakari wanda ya fada masa ya yi anfani da ita amma bata tashi ba.
Kawo yanzu yarinyar ta fara magana da bakinta bayan makwanni uku da kasa iya yin hakan. Tana asibitin IBB a Minna inda ake kula da ita. Ta ce ranar tana kan hanyarta ta zuwa kasuwa sai ta gamu da Ahmed Zakari. Ya tambayeta inda zata ta kuma fada masaamma sai ya tare hanya ya hanata tafiya. Daga bisani sai ya bata kunun zaki wanda ta sha. Tana sha sai ta kama ganin juwa kuma kirjinta na zafi ko da ta zauna sai kuma idanunta suka kama zafi kamar an samata barkono. Daga nan inda ta zauna bata kara sanin inda take ba. Tun da ta zauna kan dakalin bata sake samun hankalinta ba sai a asibiti.
Gwamnatin jihar Neja ta sha alwashin sai an hukumta matasan kamar yadda kamishaniyar harkokin mata da yara Hajiya Hassana Adamu ta sanar. Ta ce duk irin hukuncin da ya kamata a yanke masu a yi ba da bata wani lokaci ba. Idan an yi hakan wasu zasu guji aikata irin wannan ta'asar.