Wannan na zuwa ne bayan wasu mutane 781 da rundunar ta kama da laifuka a lokutan zabubuka a jihohi daban daban.
Mutanen da rundunar ta ce ta kama akan tuhumar aikata laifuka a lokutan zabe an kama su ne a jihohi daban daban kamar jihar Sokoto inda aka kama wadanda ke da hannu a laifukan da yawan su ya kai 79.
Ko bayan zabubukan rundunar ta ce an samu wasu mutane da ke fakewa da samun nasarar zabe, wajen yin murna sai su rika aikata laifuka duk da yake ba yawun jam'iyun su, suke yin hakan ba.
Wannan batun a cewar kwamishinan ‘yan sanda Muhammad Usaini Gumel sun yi bincike akan sa kuma yanzu haka batun na gaban kuliya.
Kwamishinan ya ce akwai wasu misalai na irin wadannan matsalolin da suka samu kamar a karamar hukumar Tureta inda wasu suka harbe matar wani mutum a idon ta ta amfani da danko a lokacin da suke murna, yace akwai mamaki masu murna su rike makami kamar danko har suna harbin mutane.
Hakama a cikinsu an samu ire-iren wadannan matsalolin kuma kwamishinan yace yanzu haka suna farautar wasu da ke da hannu ciki.
Yanzu da yake hukumar zaben Najeriya ta tsayar da 15 ha Aprilu a zaman ranar kammala zabubukan da basu kammala ba, a jihohin kasar, kwamishinan ‘yan sanda yace rundunar tare da sauran hukumomi na tsaro ba zasu yi kasa a guiwa ba wajen dakile duk wani yunkuri na tayar da fitina.
Da ma tun kafin gudanar da zabubukan da aka yi a 25 ga Fabrairu da na 18 ha Maris, wasu ‘yan siyasa sun amince da wanzar da zaman lafiya tsakanin magoya bayan su, kafin zabe, lokacin zabe da bayan zabe, kuma jami'an tsaron Najeriya sun lashi takobin tabbatar da hakan.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: