Daga cikin laifukan da ake zargin su da shi, sun hada da kisan kai, fyade, zamba cikin aminci, fashi da makami da wasu laifukan na daban.
Da yake wa manema labarai bayani, kakakin rundunar ‘yan sandan na jihar Borno, DSP Edet Okon ya ce wasu mutun uku an kama su ne da laifin kisan kai a kauyen Mailari, dake karamar hukumar Gubio.
Ya kara da cewa wasu mutun takwas kuma an kama su ne da laifin fashi da makami da wasu guda goma da suka fada hannun jami’an ‘yan sandan da ake zargi da satan shanu, yayin da wasu goma sha biyar ake zarginsu da satar kayan lantarki.
DSP Okon, ya nuna wa manema labarai wani dan kasar Kamaru da ake zargi da buga takardar bogi yana danfarar ‘yan gudun hijira akan cewa takarda ce da zasu karbi abinci yayin da shi kuma yake karbar kudi a hannun su.
Ya kara da cewa za’a gurfanar dasu gaban kuliya da zarar an kamala bincike.
A saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu:
Facebook Forum