Rundunar sojojin Turkiyya sun ce sun kai hari da tankar yaki ne a jiya Juma’a ga sansanonin ‘yan kungiyar ISIS da suka yiwa ruwan wuta a Arewacin Syria, amma ba gaskiyar cewa sun hari mayakan Kurdawan Syria bane wato YPG, kamar yadda YPG din suka bayyana.
Kamfanin dillancin labaran faransa ya rawaito cewa, tun a wuraren tsakiyar watan Fabrairun da ya gabata sansanin Turkawan Howitzer dake kan iyakar kasar ya ke ta ragargazar sansanonin jam’iyyar Kungiyar Dimukurayiyyar Kurdawan da ma sansanin sojinta.
Amma sojin na cewa duk a kokarin kare kai ne musayar wutar. Ko ma dai me ake ciki Amurka ta yi kira zuwa can birnin Ankara da cewa su tsagaita wuta don girmama sabuwar yarjejeniyar maida wuka cikin kube don zama lafiya.
Amma tun lokacin rahotannin na nuna cewa Turkiyya na ci gaba da harbi ruga daga nesa akan PYD din, abinda gwamnatin Ankara ta ke zargi da cewa wani reshe ne na haramtacciyar kungiyar Kurdawan PKK.