Runduna ta 7 ta mayakan Najeriya a jahar Borno, wacce take fafatawa da 'yan bindigar Boko Haram ta ceto mutane fiye da 80, galibinsu mata, daga hanun 'yan binidgar a dajin Sambisa.
Kwamandan rundunar, karkashin shirin "Operation Lafiya Dole," Manjo Janar Rogers' Nichols ne, ya bayyana haka a wani taro da manema labarai a birnin Maiduguri.
Janar Nichols, yayi amfani da taron ya karyata jita-jitar da 'yan Boko Haram din suke yadawa cewa, duk wanda ya mika wuya sojojin suna kashe su.
Tunda farko Janar Rogers yace wutar da dakarun sama na Najeriya suka yi bari a sansanin 'yan bindigar, ita ta sa suka sami nasarar gamawa da illahirin 'yan binidgar da suke wurin, kuma suka sami nasarar kubutar da wadannan mutane.
Kwamandan na Operation Lafiya Dole, yace duk dan binidgar da yake son miuka wuya, a shirye rudunar take ta karbe shi.
Daya daga cikin wadanda suka kubuta wace bata fadi sunanta ba, sai dai ta ce a dajin ita matar likitan Abubakar Shekau ne. Sunan Likitan Abu Yasir. Da Haruna ya tambayeta ko Abu Yasir din boka ne ko likitan kwarai, tace "a'a kwararre ne, domin har tiyata yana yi."
An mika mutanen ga hukumomin jahar Borno, ta hanun hukumar agajin gaggawa. Hukumar tayi alkawarin zata yi aiki domin mutanen su murmure su koma cikin al'uma.
Facebook Forum