Ana ci gaba da bayyana jimamin rasuwar fitaccen jarumi dan kasar Ingila, Roger Moore, wanda ya fi shahara a zaman dan leken asiri mai lamba 007 a fina-finan James Bond, wanda kuma ya rasu jiya talata yana da shekara 89 da haihuwa.
A jiya talata ne 'ya'yansa suka bayar da wata sanarwa suna bayyana rasuwar Sir Roger Moore a kasar Switzerland, a bayan da yayi fama na dan gajeren lokaci da cutar sankara.
Babban darektan Asusun Tallafawa Yara Na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, Anthony Lake, ya bayyana mutuwar Sir Roger Moore a matsayin "babbar hasara ga duniya ta mutumin da ya jajirce wajen kare muradun yara na duniya, yayin da dukkanmu a nan asusun UNICEF muka yi hasarar babban aboki."
Iyalan marigayin sun ce a bisa wasiyyar da ya bari, za a yi jana'izarsa a Monaco, amma ba za a gayyaci baki ba.
Moore ya shahara a fadin duniya daga shekarar 1973 zuwa 1985, a lokacin da yafito a zaman jarumi a fina-finan sanannen dan leken asiri James Bond, ko 007, har guda bakwai, cikinsu har da "Live and Let Die" da kuma "The Spy Who Loved Me."