Idan za a tuna a cikin makon nan ne babbar kotun tarayya a Abuja ta umurci shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole, ya zakuda daga mulki har sai an kammala sauraron shari’ar neman kawar da shi daga mulki.
Kwatsam sai wata babbar kotu a Kano ta sake yanke wani hukuncin da ya soke umurnin kotun ta Abuja.
Hakan dai ya haddasa muhawara kan yadda kotuna biyu masu hurumi daya za su yanke irin wadannan hukunce-hukuncen da ke cin karo da juna.
Lauya mai zaman kansa Barista Ibrahim Bello ya ce dole a jira sai kotun Abuja ta kammala sauraron karar.
Ya fadi hakan ne a yayin wata hirar da ya yi da wakilinmu Nasiru Adamu El-Hikaya.
A cewarsa “daukar wata shari’a, a je a kara yin ta a Kano, hakan ba zai taba yiwuwa ba. Ko da kotun koli aka je, sai an sake waiwayen inda aka fara shigar da karar, wato kotun da ke Abuja.”
Daya daga wadanda su ka shigar da karar kalubalantar Oshiomhole, kuma jigon APC a Zamfara, Sani Gwamna, ya ce hukuncin kotun Kano bai shafe su ba.
Shi kuma sakataren walwala na APC Ibrahim Masari na nuna kwarin gwiwar Oshiomhole ke turbar nasara.
Ya ce "dole ne jami'an tsaro su ba shugaban jam'iyya tsaro har sai an gama wannan dambarwar."
A yanzu dai an zuba ido a ga yadda lamarin zai kasance a hedikwatar jam’iyyar, ko Oshiomhole na iya shiga ofis ko a hana shi.
Saurari wannan rahoton a sauti daga bakin wakilinmu Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum