Wannan na faruwa ne bayan hukuncin wata babbar kotun a Abuja da ya umurci shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole ya koma gefe har sai an kammala sauraron karar neman kwabe shi daga mulki.
Ba mamaki hukuncin kotun tarayya a Kano da ya marawa barin Oshiomhole baya ya zauna a gado bai yi tasiri a zahiri ba.
Lauya mai zaman kan sa, Barista Ibrahim Bello, ya ce kara ta biyu tamkar keta haddin kotu ne.
A bangaren masu kara a Abuja, mukaddashin sakataren jam’iyyar APC, Victor Giadom, ne ya cancanci zama mai rikon kwaryar shugabancin jam’iyyar har sai an kammala shari’a.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu, ya sanar da nada Waziri Bulama daga jihar Borno a matsayin sakataren jam’iyyar.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa maso gabas, Mustapha Salihu, da ke kan gaba a shari’ar, ya ce Oshiomhole ya dau matakin cike gurabe ta fargar jaji bayan an dakatar da shi daga mulki.
Sakataren walwalar jam’iyyar Ibrahim Masari da ke marawa Oshiomhole baya, ya ce da hannun su aka rufe helkwatar jam’iyyar don hana tarzoma.
Sai dai wani abin da ke nuna ta’azzarar lamarin shi ne kiran da masu marawa Adamas baya su ka yi wa shugaba Buhari ya sa baki.
Ana ganin dai shugaban da aka dakatar yana cikin tsaka mai wuya, inda tsohon shugaba jam’iyyar John Odigie ya yada kwallon mangoro.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:
Facebook Forum