Inji Gwynn Stevens, shugaban kanjamau na kasar Afrika ta kudu, "Akwai yawan rubuce rubuce da suka nuna cewa mun kusan zuwa ga karshen cutar kanjamau, ama wanan ba dai dai bane domin akwai sauran aiki wajen neman rigakafi na sannani.”
Koda yake an cigaba sosai a yaki da cutar kanjamau, masana da likitoci suna kan fama da bambancin al’adu da kuma bambancin dokoki, bisaga wata takarda da aka rubuta a jaridar magani, New England Journal.
Masana sun bayyana cewa halayen mutane shine babban kalubale ga aikin kawas da cutar. Ci gaba zai tabata idan mutane sun sa kai tare da masanan kiwon lafiya ama yawancin mutane basuwa nuna karfin hali, inji Anthony Fauci, direktan makarantar gane cututtuka a Amurka.
Yanzu wata hanyar da ake bi wadda ta hada da bai wa mutane magani wadanda basuwa da cutar kanjamau ba domin kiyaye kamuwarsu da cutar shima yana da amfani idan mutane sun mai da hankali su yi yada ya kamata, Inji Fauci.
Ya kuma ce, harkokin al’ada da doka suna hana nasarar rigakafin kanjamau. A misali, a kasashe fiye da 70 inda jima’i tsakanin namiji da namiji ba a yarda ba, yana dawuya samun maza masu wannan tabi’a domin shawara da kuma yin magani, Fauci ya kara fadi.
Shi kuma Steven yace: "Ba zaka taba samin wani ba da zai zo domin gwaji, bayan da an basu tsoron kurkuku ko kuma mutuwa gaba daya."