Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ribar Da Ke Cikin Noman Alkama Ba Ta Misaltuwa – Ministan Noma Kyari


Ministan noma na Najeriya Abubakar Kyari
Ministan noma na Najeriya Abubakar Kyari

Ministan noma na Najeriya Abubakar Kyari ya ce ribar da ke cikin noman alkama ba ya misaltuwa don abubuwan da a ke samarwa daga alkamar na da yawan gaske.

Wannan na daga bayanan da ministan ya gabatar a taron zantawa na zauren noma na shugaban Najeriya a Abuja.

Abubakar Kyari ya baiyana cewa da duk manoma sun san arzikin da ke cikin noman alkama abun da za su tsaya a kai kenan.

Kazalika ministan ya ce ya zama mai muhimmanci a kawo iri mai inganci don samun yabanya mai yawa ya na mai misali da yanda a dan karamin fili kadada biyu a ke samun ton 10 na masara a Masar.

Babban manomi Alhaji Isa Tafida Mafindi da ke cikin mahalrta taron ya `ce in an yi amfani da kwararru za a cimma wannan nasarar mussamman daidai lokacin da shigo da abinci daga ketare ke shafar farashin albarkatun noma na cikin gida.

Taron ya ba da shawarar tallafawa manoma da na’urorin noma masu amfani da hasken rana wajen noman rani, ba da lamuni mai saukin biya da kuma sayan amfanin gonan daga hannun manoman.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG