Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rex Tillerson Na Amurka Zai Gana Da Nato


Jami’ai a Amurka sunce Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson zai gana da mambobin gamayyar NATO a sati mai kamawa, bayan kalubalantar matsayar sa ta kaucewa taron tattaunawa na Ministocin waje na NATO.

Jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurka sunce Tillerson zai hadu da mambobin a ranar 31 ga watan Maris a Brussels. Ministocin wajen Nato daga kasashen da aka shirya da farko domin ganawar zasu hadu a Brussels ranakun 5 da kuma 6 ga watan Afrilu. Babu cikakkiyar masaniyar ko sabuwar ganawar zata maye gurbin ta kwanakin watan Afrilun.

Babu wani bayani na musanman daga NATO.

A farkon satin da ya gabata ne, ofishin Tillerson yace ba zai samu damar halartar zaman tattaunawar na watan Afrilu ba na gamayyar Mambobi 28, wanda ya tada wasu wasin mai da kan Gwamnatin Amurka akan NATO.

Shugaban kasa Donald Trump ya sha nanata cewar NATO bata da wani amfani, duk da dai Mataimakin shugaban kasar Mike Pence ya furta goyon bayan Amurka da kawayenta yayin taron manema labarai a Brussels a watan da ya gabata haka shima Tillerson ya bayyana goyon bayansa ga NATO kamar yadda Sakataren Harkokin Tsaron Amurka James Mattis shima ya nuna.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG