Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tana samun koma baya a wasanninta da take bugawa, musamman na gasar Laliga ta bana.
A ranar Lahadi da ta gabata Real Madrid tasha kashi a hanun takwararta Real Sociedad da ci 2-0 a Santiago Bernabeu, a wasan mako na 18.
Masu fashin baki kan wasannin kwallon kafa na ganin cewar idan kungiyar taci gaba da rashin samun nasara a wasanninta na gaba, to zata iya rasa tikitin shiga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai na shekarar 2019/2020, domin a ranar 3 ga watan Janairun 2019, sunyi canjaras da Villarreal 2-2.
Real Madrid, dai a yanzu tana mataki na biyar da maki 30 a teburin Laliga mako na 18, banbancin maki 4 tsakanita da Real Betis, da take mataki na shida da maki 26.
Bayan haka akwai tazarar maki Goma tsakanita da Barcelona wace take saman teburin, Madrid ta buga wasan ne ba tare da dan wasan gabanta ba, wato Gareth Bale sakamakon yana fama da jinya a kafarsa.
Sai dai dan wasanta kuma gwarzon dan kwallon duniya na shekarar 2018 Luka Modric, yace ko kadan wannan rashin nasa ba ya basu tsoro, domin zasu dawo kan ganiyarsu a wasannin gaba, a ranar 13 ga watan Janairu 2019, kungiyar ta Real Madrid zata kai ziyara wa Real Betis, a wasan mako na 19 bangaren Laliga ta kasar Spain.
Facebook Forum