Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Na Iya Lashe Gasar Laliga na 2016/17


A cigaba da karasa wasu wasanni da akeyi a bangaren laliga na kasar Spain da kuma bangaren Firimiya na kasar Ingila na shekara 2016/17, na wasu makonni da ba'a samu damar bugawa ba saboda wasu dalilai jiya kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, ta samu nasara akan Sunderland, da,ci 2-0,

Manchester City, ta doke Westbromwich, da kwallaye 3-1 a wasansu na mako na 34.

A yau kuma Southampton, zata kara da Manchester united, a wasan mako na 28 da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar da kamaru.

A can kasar Spain, shima akwai wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Celta Vigo, da Real Madrid, a wasan mako na 21 a bangaren laliga na bana damisalin karfe takwas na dare agogon Najeriya da Nijar.

Idan Real Madrid, ta samu nasara a wannan wasan zata Koma matsayi na daya a saman teburin laliga, inda hakan zai iya bata karfin guiwar lashe gasar na 2016/17.

Sai dai yanzu haka Real Madrid, tana mataki na biyu ne da maki 87 ita kuwa abokiyar hamayyarta Barcelona, tana saman teburin ne a mataki na daya, itama da maki 87 inda take da sauran wasa daya tak, ta kammala. Real Madrid kuwa tana da sauran wasanni biyu ne duk da wanda zata kara a yau tsakaninta da Celta Vigo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG