Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Aiki Ga Mata A Ghana Ya Sa Wata 'Yar Sa Kai Koyar Da Mata Sana'ar Ado Da Kwalliya


Sana'ar kwalliya
Sana'ar kwalliya

Wani rahoto da hukumar kididdiga ta kasar Ghana ta fitar ya nuna cewa mutum miliyan 1.7 ne basu da sana'ar yi kafin karashen rubu'i na uku na shekarar 2022, yayin da kuma kashi biyu cikin uku mata ne.

Fauziya Adam mai fafutukar kare hakkin mata a Ghana na ganin mata ne ya kamata a fi maida hankali sosai a kan su saboda irin gagarumar gudunmuwar da suke bayarwa a fagen kula da gida da kuma ci gaban kasa baki daya.

Sana'ar kwalliya
Sana'ar kwalliya

"Gaskiya wannan rahoto da hukumar kididdiga ta fitar ya sanya mu cikin halin damuwa sosai saboda mu mata akwai gudunmuwar da mu ke bayar wa a gidajenmu da ma kasa baki daya. Har idan an sami cikas wajen aikin mazajenmu, ko shakka babu mu mata ne ke daukar dawainiyar gida da kula da neman ilimin yara. Idan mata suna jagorantar masana'antu to ana samun ci gaba fiye da maza, don haka idan mace bata da aiki to za'a fuskanci matsala sosai" inji ta.

Sana'ar kwalliya
Sana'ar kwalliya

Mataimakin ministan kwadago ta kasa da ya halarci taron gabatar da rahoton, ya bayyana gamsuwarsa tare da cewa gwamnati za ta yi kokarin daidaita jinsi musamman ta fannin samar da sana'o'i a kasar domin cika burinta na ba da gudunmuwa wajen ci gaba mai dorewa.

To sai dai a wani bangare na ba da tata gudunmuwa wajen shawo kan matsalar rashin daidaiton jinsi ta fannin sana'o'i a kasar, wata mata Najat Adam mai aikin sa kai ta fara horar da mata aikin ado da kwalliya domin ganin sun yi dogaro da kai.

Najat Adam ta fadawa muryar Amurka cewa "ni da kaina da na taso ban da sana'ar yi, amma da na koyi sana'ar ado da kwalliya sai na ga yana da anfani sosai, a nan nike ba da gudunmuwar koyar da su matasan domin su kuma suyi dogaro da kai."

Wasu mata da suka amfana sun ce wannan sana'ar da suka koya za ta taimaka musu da ma wasu masu tasowa nan gaba.

Ita kuwa Shamsiya Issah da aka yaye cewa tayi "ni ma an yaye ni don haka so nike in bude shago in taimaka wa mata da ba su da aikin yi su kuma su samu kudi."

A halin yanzu Najat Adam ta yaye daliban da ta horar da su sana'ar su fiye da dari da hamsin, kuma tana fatar ta sami mata masu yawan gaske su kama sana'ar hannu domin yin dogaro da kai.

Saurari rahoton Hamza Adam:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

XS
SM
MD
LG