Rashin hadin kai a bangaren masu shirya fina-finai na daga cikin babban kalubalen da ke ci wa masana’antar Kannywood tuwo a kwarya, in ji furodusa Iliyasu Abdulmumin.
A cewar Abdulmumin, wanda aka fi sani da Tantiri, duk da cewar suna da kungiyar masu shirya fina-fina, masana’antar ta Kannywood na fama da matsalar rashin jajirtattun da za su tsaya tsayin daka domin tabbatar da ci gabanta.
A cewar shi, sunan Tantiri da ake kiransa, ya samo asali ne a wani fim dinsa da ya fara wanda ya samu wannan lakabi na Tantiri.
Abdulmumin ya kara da cewa masana’antar ta Kannywood ta same shi da sana’arsa ta kamara yana mai cewa da shi aka kafa masana’antar.
Ko da ya ke Tantiri ya ce ya fara harkar fim ne da rubuta labari, inda daga bisani sai ya rikida ya koma aikin furodusa, yana mai cewa yakan yi rubutu ya kuma ba da umarni a fagen daukar hoto, a wasu lokutan ma har ta kai shi fitowa a matsayin jarumi.
Kamar kowa, Tantiri ya ce sha’awa ce ta ja shi harkar fim, inda ya ce ya fito a cikin fina-finai kamar Tsumbuka, Gagare da Tantiri da dai sauransu.
Daga cikin abin da ke ci masa tuwo a kwarya a cewar Tantiri, shi ne yadda har yanzu Hausawa suka ki ya amince da sana’ar fim kamar yadda ya kamata.
Jarumin na fim din Tantiri ya kuma ce, kungiyar da ke tattara masu shirya fina-finai na da wasu matsalolin da har yanzu ba ta magance su ba, inda ya ce akwai matukar muhimmanci su hada kawunansu domin kawo gyare-gyare da zai bunkasa wannan masana’anta ta Kannywood.
Facebook Forum