Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Baiwa Malamai Dama Yana Kawo Cikas Wajan Koyar Da Dalibai


Maryam Mohammad Malamar Makaranta
Maryam Mohammad Malamar Makaranta

Rashin baiwa Malamai damar da yakamata wajen koyarwa da tsawatar da yara a makarantu da hukumomin makarantu ke yi masamman makarantu masu zaman kansu yana jawo koma baya wajen cimma burin malamai na ilimatar da yara da basu tarbiyar da ta dace.

Wata malamar makaranta Maryam Mohammad, ce ta furta haka a wani hira da wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir a birnin Kano.

Ta kara da cewa baya ga yar matsalolin hukumomi makaranta wani zubin ma akan samu ‘yar kalubale daga wasu daga cikin iyayen dalibai inda da zarar an tsawatar da ‘yayansu sai iyaye su zo suna korafe korafe.

Mafi yawan iyayen basa damuwa da cewar malami na kokarin hukunta ‘yayan nasu ne domin basu tarbiya, inda suma a nasu bangaran na hukumomin makaranta kan tsawatar da malaman da suka tsawatarwa daliban ta hanyar hukunta su.

Maryam ta ce wadan su makarantu suna yin hakan ne kasancewar makarantar ta kudi ce kuma basa son bata wa iyayen yaran rai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

XS
SM
MD
LG