Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Aikin Yi Zai Karu a Najeriya


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A wani bincike da hukumar kidigdiga ta Najeriya tayi tace rashin aikin yi zai karu a kasar daga yanzu har zuwa shekara mai zuwa.

Hukumar kidigdiga ta sanar cewa rashin aikin yi zai karu a Najeriya daga yanzu har shekara mai zuwa musamman cikin matasa.

Kamar yadda hukumar ta bayyana rashin aikin yi zai karu ne da wajen kashi biyu cikin dari akan lamarin da ake ciki yanzu. Hukumar tace a shekarar 2011 rashin aikin yi kashi 23 ne cikin dari. Amma adadin ya haura a shekara 2013 zuwa kashi 29 cikin dari. Wato cikin shekaru biyu kacal an samu kari da kashi shida cikin dari duk da kokarin da gwamnatoci ke ikirarin yi na samar ma matasa aikin yi.

Sabili da haka matasan arewa maso gabas sun kira gwamnatocinsu da su kara karfi da karfe wurin kirkirowa matasansu aikin yi idan har ana son a shawo kan tababarewar harkar tsaro a yankin.

Yayin da matasan suke daukar jarabawar shiga aikin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Najeriya, sun shaidawa wakiliyar Murya Amurka cewa samar masu da abun yi kadai zai magance tashin tashinar da kasar ke fama da ita. Wata matashiya tace rashin aikin yi na sa mutane yin tunane daban daban da na banza da aikata aikin asha. Wani yace mutane nada yawa. Akwai bukatar kara ayyuka domin mutane da yawa su samu abun yi. Wani ya kara da cewa rashin aiki yasa wasu suna tunanen aikata muggan ayyuka.

Duk da cewa mutane dari shida da 'yan kai hukumar ta gayyata daga jihohi shida na arewa maso gabas domin su rubuta jarabawar fiye da mutum dubu suka yi dafifi a wurin jarabawar.

Ga rahoton Sa'adatu Fawu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG