Rasha na kiran Amurka da ta sake tunani, game da umurnin da ta bayar na rufe wasu gine-ginen diflomasiyyar Rasha guda uku, ta na mai bayyana rufe gine-ginen da, abin da ta kira, "matakin neman tsokana."
"Mu na daukar abin da ya faru a matsayin wani matakin janyo cece-kucce muraran, kuma wata babbar sabawa dokar kasa da kasa ce Amurka ta yi," a cewar Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha a wata sanarwar da ta bada jiya Lahadi.
"Mu na kira ga hukumomin Amurka da su shiga hankalinsu su maida ma Rasha gine-ginen diflomasiyyarta ba tare da bata lokaci ba, ko kuma Amurka ta zama ita ke da duk wani laifin tabarbarewar dangantakarmu da ita," a cewar Rasha.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fada ranar Asabar cewa ta kwace wadanan gine-ginen diflomasiyya uku da Rasha ta fice daga cikinsu, kamar yadda gwamnatin Amurka ta umurta.
Facebook Forum