Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Zazzabin Cizon Sauro Ta Duniya 2021


The White House
The White House

Ranar 25 ga Afrilu ita ce Ranar Zazzabin cizon sauro ta Duniya, wata damata wayar da kan jama'a game da wannan cuta mai saurin kisa da kuma sabunta tallafinmu ga Burin Majalisar Dinkin Duniya mai dorewa na kawo karshen annobar zazzabin cizon sauro nan da shekarar 2030.

A yau, wannan cutar da za a iya kiyayewa da magancewa na ci gaba da kashe rayuka da yawa a duniya. A shekarar 2019, kimanin mutane miliyan 229 a duniya sun kamu da zazzabin cizon sauro kuma 409,000 sun mutu. Daga ciki, kashi 67 cikin 100 yara ne ‘yan kasa da shekaru biyar.

Koda yake kusan rabin yawan mutanen duniya na fuskantar barazanar zazzabin cizon sauro, Afirka kudu da Sahar tana da kashi 94 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar da kuma mace-mace, saboda mummunar kwayar cutar da aka samu a wurin.

Duk da haka, halin da ake ciki na ci gaba da inganta a hankali tun daga farkon karnin, godiya ga kwazo da ake yi don ci gaba da yaki da sauro, da rigakafin cizon, da magungunan cutar zazzabin cizon sauron.

A wannan shekara, bikin ranar zazzabin cizon sauro na duniya zai hada da bikin nasarorin da kasashen suka samu, har ma da cimma nasarar kawar da zazzabin.

Tabbas, bisa ga Rahoton zazzabin cizon sauro na Duniya na 2020, shekarun da suka gabata sun nuna nasarar da ba a taɓa gani ba a duniya game da zazzaɓin cizon sauro, duk da mahimman ƙalubalen da ke tattare da juriya na maganin zazzabin cizon sauro da kuma COVID-19.

Misali, a cikin shekaru 20 da suka gabata, shida daga cikin kasashen da ke fama da tsananin matsallar a yankin na Mekong sun ga cewa cutar ta su ta ragu da kashi 97 da kuma mutuwar zazzabin da fiye da kashi 99.

Tabbas, a shekarar 2019, kasashe 27 sun bada rahoton 'yan asalin yankin guda 100 wadanda suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro, daga kasashe 6 a shekarar 2000. Yanayin da ake ciki zai ci gaba da inganta, amma sai da nufin yunkurin za a kawar da wannan annoba, da kudaden da ake bukata don yaki da ita.

Kasar Amurka ta fi kowace kasa bayar da gudummawa, don magance cutar zazzabin cizon sauro, da kuma kawar da ita, a duniya. A cikin shekarar kasafin kudi ta 2021, tallafin da kasashen biyu suka bayar don magance cutar zazzabin cizon sauro da ayyukan bincike ya kai dala miliyan 979.

Bugu da kari, Amurka ita ce babbar mai bayar da tallafi ga Asusun Duniya don Yaki da cutar kanjamau, tarin fuka da zazzabin cizon sauro, wanda ke samar da sama da kashi 50 cikin 100 na duk kudaden kasa da kasa na shirye-shiryen zazzabin cizon sauro. Duk da haka, idan za a shawo kan zazzabin cizon sauro, ana bukatar ƙara damara.

A cikin kalaman Dr. Anthony Fauci, Daraktan Cibiyar Kula da Cututtuka masu yaduwa na Amurka kuma babban likita mai ba da shawara ga Shugaba Joseph Biden, “Sai dai idan muna son mu fuskanci dagewa har ma da sake bullar zazzabin cizon sauro a karni mai zuwa da bayansa, wajibi ne mu ci gaba da ƙudurinmu na kawar da wannan annoba a duniya baki ɗaya. Abu ne maiyuwa. ”

XS
SM
MD
LG