Ranar 13 ga watan Fabrairu ta kowace shekara, rana ce ta bikin ranar rediyo ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin ranar Rediyo ta duniya.
Ranar Rediyo ta Duniya, rana ce da aka kebe don duba tasirin da radiyo ke da shi wajen inganta rayuwar jama'a.
A ko da yaushe, gidajen rediyo kan bayar da dama ga jama'a domin fadin albarkacin bakinsu da kuma sanar da su irin wainar da ake toyawa a duniya ta kowane fanni na rayuwar dan Adam - walau ta fannin samar da labaru da dumi-duminsu, wadanda ke tsage gaskiya komi dacinta.
Wasu ma'abuta rediyo a Adamawa sun bayyana yadda su ke amfana da jin rediyo kullu yaumin. Wani mai suna Salisu Abdulmuminu Abba ya ce rediyo na da matukar muhimmanci wajen wayar da kai da kuma nishadantarwa. Shi ma Salman Yayaji Yusuf ya ce rediyo na matukar taimaka ma al'umma.
Wani dattijo mai suna Mallam Aliyu Usman ya ce ya shafe fiye da shekaru ashirin yana sauraran radiyo,kuma ya bayyana yadda rediyo ke fadakar da shi da kuma ilmantar da shi da sauran jama'a..
Baba Iyali Kawu dake zama shugaban wata kungiyar sa kai dake kula da shirye-shiryen kafofin yada labarai ta Media observers ya bayyana muhimmancin rediyo.
Ga wakilinmu a Adamawa Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:
Facebook Forum