Yau take babba rana a tarihin dan’adam a duniya, Majalisar Dinkin Duniya, ta ware ranar 10 ga watan Disamba a matsayin ranar tunawa da hakkin dan’adam a duniya. Don duba fai’dar wannan ranar, wasu ‘yan Najeriya sun bayyana ra’ayinsu dangane da hakan.
Sun yi korafi kwarai da gaske dangane da take hakin bil’ada da ake yi a Najeriya, wanda suke cewar dan’adam bai da wani hakki, saboda duk wani abuda yakamata ace dan’adam ya mallaka a rayuwar nan su basu ganshiba. Saboda a makarantunsu babu wani abu na more rayuwa da zakace gashi ansamar ma dalibai. Sun kuma yi nuni da cewar alokutta da dama idan kayi kokarin ka nemi yancin naka, sai a nuna maka cewar baka da shi don haka dan’adam bai da wani yanci.
Sun kuma kara da cewar wasu kasashe da basu kai Najeriya arziki ba da cigaba, amma mutane wadannan kasashen suna da yanci. Abun takaici shine shi talaka bashida hanyar da zai karbar ma kansa yanci. Hasalima mata ba’a basu hakkokinsu da yakamata, wasu mazajen basu ba matansu damar yin karatu kowani abu na cigaban kansu. Wani malamin Dr. Mustapha Hussain Isma’il yayi muna Karin haske dangane da hakkin dan’adam a addinance. Yace Allah ma ya halacci dan’adam kuma yaba shi damar yin walwala, yanci da yadda zai bauta masa batare da ya saba masa ba.