Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

RAHOTO NA MUSAMMAN A KAN BOKO HARAM: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi (Babi na 1)


Tashin bam da ya kashe mutane akalla 15 a sananniyar kasuwar nan da ake kira Monday Market a Maiduguri ranar 1 Yuli, 2014, na daya daga cikin tashe-tashen bama bamai da suka addabi yankin arewacin Najeriya. (AFP)
Tashin bam da ya kashe mutane akalla 15 a sananniyar kasuwar nan da ake kira Monday Market a Maiduguri ranar 1 Yuli, 2014, na daya daga cikin tashe-tashen bama bamai da suka addabi yankin arewacin Najeriya. (AFP)

Kashe-kashe da zub da jini da tashe-tashen hankula sun zamo ruwan dare a yankin arewa maso gabashin Najeriya a dalilin hare-haren ‘yan Boko Haram. A yayin da wannan tashin hankali ke bazuwa zuwa wasu sassan na Najeriya, har ma da makwabtanta, fargaba tana kara yawaita cewa watakila gwamnatin Najeriya ba ta san yadda zata takali wannan batu ba. Ko kuma tana kara rura wutar fitinar ne ma da kanta.

A daidai lokacin da aka fara ganin soja na farko ya sa wuka zai yanka mutum na farko a hoton bidiyon nan, akwai gawar mutum guda cikin ramin da aka tona, da kuma jini a bakin ramin daga inda aka yanka shi. A bayansu, akwai mutanen dake zaune a layi kafin a zo kansu.

Wannan bidiyo da aka dauka da wayar salula a karshen watan Mayu na 2014, ya nuna wasu mutane uku, sanye da kayan soja irin na sojojin Najeriya, wasu rike da bindigogin Ak-47 da adduna, tare da wasu mutanen biyu sanye da kayan farar hula. An nuna yadda aka yanka mutane uku a cikin wannan bidiyon. An yi imanin cewa wadanda aka yanka a wannan hoton bidiyo, ko dai ‘yan Boko Haram ne, ko magoya bayansu, ko kuma dai watakila ma fararen hular da ba su san komai ba. Alamu sun nuna sojojin dake cikin bidiyon, sojojin gwamnatin Najeriya ne.

Wani sojan dake aiki a sabuwar shiyya ta 7 ta rundunar sojojin Najeriya da aka dora ma alhakin yakar ‘yan Boko Haram, shi ne ya ba VOA wannan bidiyon. Sojan ya bayyana wannan bidiyon, da wasu makamantansa da ya ba VOA a zaman misali na daya daga cikin hanyoyin da suke bi wajen yakar barazanar ‘yan Boko Haram, abinda ya kira “Hanyar Soja” ko “Military Way” kamar yadda ya fada a turance.

Shekaru biyar a bayan fara wannan rikicin, Najeriya tana jin jiki. Irin kashe-kashe da zub da jini da kuma tashe-tashen hankulan da tun farko ake ganinsu a yankin arewa maso gabas inda ake fama da talauci, yanzu ya bazu. A yanzu, kungiyar Boko Haram tana fitowa fili tana kalubalantar gwamnatin Najeriya, a yunkurinta na shimfida abinda a cewarta, shi ne tsarin Shari’ar Musulunci. A mako gudan da ya shige kawai ma, mayakan Boko Haram sun kwace garuruwan Gulak, da Michika a Jihar Adamawa, bayan da suka kwace garuruwan Gwoza, Bama da Madagali, kwanaki kafin wannan. A yanzu, kullum sai an samu labarin harbe-harbe ko fashe-fashe ko kashe-kashe a wurare da dama a kasar, yayin da aka kai hare-hare da dama a Abuja, babban birnin kasar, na baya-bayan nan a ranar 25 ga watan Yuni. A cikin wannan shekara kawai, an kashe mutane fiye da dubu biyu, yayin da wasu dubun dubata suka gudu daga gidajensu ala tilas a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kamar a Damboa, Gwoza, Bama, Chibok, Buni Yadi, Gujba da wasu daruruwan garuruwa da kauyuka na yankin.

Babban Masallaccin da ake ginawa a Maiduguri yana kusa da wata unguwa da 'yan Boko Haram suka rike na wani dan lokaci daga 2012-2013. (VOA/Ibrahim Ahmed)

Irin martanin da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya take maidawa, ya kasa tabuka wani abin a zo a gani har yanzu. Cin hanci da rashawa yayi yawa sosai a cibiyoyin gwamnatin Najeriya, musamman a tsakanin hukumomi da ma’aikatun tsaro in ji wasu sojojin da suka yi magana da VOA a kan wannan. Haka kuma, an fara bayyana tababa a kan ko jami’an tsaron na Najeriya zasu ma iya tabuka wani abu, ko za a ba su sukunin tabuka wani abu, a bayan da aka kasa kwato dalibai mata ‘yan makaranta su fiye da 200 wadanda ‘yan Boko Haram suka sace kiri da muzu daga garin Chibok a Jihar Borno.

Wani dan sandan dake aiki a rundunar JTF a Jihar Borno, ya fadawa VOA cewa harsasai 30 ake ba su idan zasu fita aikin sintiri. Idan su na son a ninka musu zuwa 60 sai sun bayar da cin hanci ga mai raba musu makamai.

“Ta yaya zaka iya yakar abokin gabar da ya tinkare ka da harsasai fiye da dubu a jikinsa?” in ji wannan dan sanda.

Kwararru da masana daga ciki da wajen Najeriya da dama su na kara nuna damuwar cewa irin matakan da jami’an tsaron Najeriya suke dauka na kashe wadanda ake zargi, da sace su, ko kuma kamawa da daure mutum haka siddan, a yakin da suke yi da Boko Haram, yana kara munin wannan al’amari ne ta hanyar kara tsoratarwa da cin zarafin fararen hular da tun farko su na yin dari-dari da sojojin, sannan yana kara sanya su su na tausaya ma ‘yan bindigar. Wani rahoton da kungiyar Amnesty International ta bayar kwanakin baya ya nuna shaidar kisa ba ta hanyar shari’a ba, da wasu munanan ayyukan keta hakkin bil Adama da sojojin Najeriya suke aikatawa a arewa maso gabashin Najeriya.

A yanzu dai, dukkan kasashen dake makwabtaka da Najeriya a arewa, musamman Kamaru, Nijar, Chadi da sauran sassan yankin Sahel su na cikin hatsari na wannan tayar da kayar bayan Boko Haram.

Peter Pham, kwararre kan harkokin Najeriya a wata cibiyar bincike da ake kira Atlantic Council dake Washington, yace, “Abinda ya faro a zaman wata matsalar wani yanki na cikin gida yanzu ya rikide ya koma matsala ga duk kasar da makwabtanta.”

Cibiyar wannan tayar da kayar baya dai, har yanzu tana inda ta faro ne, watau a birnin Maiduguri: birnin da a yanzu zullumi da fargaba suka rufe jama’a cikinta.

Karin Bayani akan Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG